Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta bayyana cewa tana cikin shiri tsaf don karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf idan ya yanke shawarar barin jam’iyyar NNPP zuwa APC.
A wata sanarwar manema labarai da shugaban jam’iyyar na jihar, Abdullahi Abbas, ya fitar, APC ta ce matakin zai iya kawo wa jihar Kano ci gaba mai ɗorewa da haɗin kai tsakanin ’yan siyasa.
Abdullahi Abbas ya ƙara da cewa gayyatar da jam’iyyar ke yi wa gwamnan ba ta da alaƙa da gaba ta siyasa, illa dai manufar gina Kano ɗaya mai ci gaba, tare da tabbatar da cewa idan gwamnan da manyan ’yan NNPP suka shigo APC, za a tarɓe su cikin mutunci da girmamawa a ƙarƙashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
