Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a ofishinsa da ke fadar shugaban ƙasa, Abuja.
Gwamnan wanda ya isa fadar da misalin ƙarfe 4:10 na yamma, yana sanye da farar babbar riga da hula ja, ya shiga ganawar da ake ganin ba ta rasa nasaba da jita-jitar sauya shekarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
