Kasancewarsa gogaggen Dan siyasa da ya shahara ta fuskoki daban – daban, bayan da ya rike mukamai da dama wannan kadai ya Isa yasa ya zama shugaban jam, iyyar Apc na Jihar kano, Hon kawu Idris Hausawa.
wani Mai sharhi Akan AL, amuran siyasa kwamared murtala Lisa ya bayyana hakanne lokacin da ya Ke ganawa da jaridar muryar Arewa Ayau. Com ya bayyana cewar Hon kawu Idris Hausawa mutum ne da baya daga kafa wajen nemowa jam, iyyar Apc hakkinta a ciki da wajen Jihar kano.
Murtala Lisa ya Kara da cewar lokaci yayi da yayan jam, iyyar Apc zasu Bude idanu suga irin tallafin da Hon kawu Idris Hausawa yake baiwa AL, umma batare da nuna banbanciba.
Kawu Hausawa yana da alaka Mai kyau da shugabannni jam, iyyar Apc na kasa har da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, Wanda hakan na nuni da kwarewarsa wajen mu, amala Mai kyau a tsakanin Al, umma.
Lisa yace Ana iya cewa idan kawu Idris Hausawa ya fito tamkar Rana ce da tafin Hannu bazai iya kare taba.
Murtala Lisa ya Ja hankalin yayan jam, iyyar Apc na Jihar kano su cigaba da baiwa Hon kawu Idris Hausawa hadin Kai da goyan baya domin kaiwa ga gaci
