An kafa wani tsari na musamman na haɗa kowa da kowa bisa ka’idar “Hana Wani, Hana Kai”, wato babu wanda za a ware, babu wanda za a hana dama.
Bisa wannan ka’ida, Hon. Doguwa ya sanar da cewa sababbin mambobin jam’iyyar APC da suka sauya sheƙa daga NNPP, sakamakon kiran da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi, an shigar da su da cikin shirin tallafi da ƙarfafa al’umma na samar da Sana, oi (empowerment).
Ya ce:
“Mun tanadi wani kaso na wannan gagarumin shirin tallafi ne musamman domin sababbin mambobinmu da suka amsa kiran gwamna suka shiga APC. Za su amfana ƙwarai da gaske daga waɗannan tsare-tsare.”
Dan majalisar, wanda ya bayyana kansa a matsayin jagora kuma ‘kwamandan’ tafiyar siyasa a mazabar Doguwa/Tudun Wada, ya nuna godiya ga Allah bisa ni’imar ganin sabuwar shekarar 2026, tare da jaddada ƙudurinsa na ci gaba da ƙarfafa haɗin kai, shigar da kowa cikin al’amura, da cigaba.
Kamar yadda Mai magana da yawun Rt Hon Alhassan Ado Doguwa ya wallafa a shafin sa Auwal Ali Sufi utai (SLA) Haka kuma, ya yi maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC, yana masa fatan samun zaman lafiya, nasara, da shiriya daga Allah bisa jagorancinsa na gwamnatin Kano, da kuma Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin APC wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ke jagoranta.
Doguwa ya ce:
“Allah Ya sanya alheri da farin ciki a dukkan al’amuran gwamnatin APC a Jihar Kano da kuma gwamnatin tarayya ta Najeriya ƙarƙashin APC.”
Wannan sanarwa ta samu karɓuwa sosai daga mambobin jam’iyya da shugabannin al’umma, inda suka bayyana shirin tallafin a matsayin ɗaya daga cikin manyan tsare-tsaren da suka taɓa shafar jama’a kai tsaye a tarihin mazabar Doguwa/Tudun Wada.
Rt. Hon. Alhassan Ado Doguwa na daga cikin fitattun ‘yan majalisar dokoki mafi ƙwarewa a Majalisar Tarayya ta Najeriya, kuma fitaccen murya ne wajen haɗa kai a siyasa, tallafa wa jama’a a matakin ƙasa, da ƙarfafa zaman lafiya a jam’iyya.
Yayin da a karshen taron da aka gudanar a gidan Gwamnatin Jihar kano wajen karbar gwamna Abba Kabir Yusuf Rt Hon Alhassan Ado Doguwa sardaunan kasar hausa Mai tuta ya rufe taro da Addu, a wannan na nuni da cewar Rt Hon Alhassan shine kyauren jam, iyyar Apc na kudancin kano, Kamar yadda Sufi ya bayyana
