Kungiyar ’Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa karkashin jagorancin shugabanta, Ismail Ibrahim Dutse, ta ce ta gudanar da rabon tallafin kudi domin rage wa mambobinta radadin hidimar bukukuwan Sallah.

Arewa Albishir ta rawaito cewa, Shugaban kungiyar ya bayyana cewa, a watan Azumin Ramadan daya gabata ma kungiyar ta gudanar da irin wannan tallafi ta hanyar rabon kudi da kayan abinci ga iyalan mambobin da suka rasu da kuma wadanda suka yi ritaya.

 

Ya ce shirin na daga cikin kokarin kungiyar na tallafawa walwala da jin dadin mambobinta musamman a lokutan bukukuwa da kuma lokutan bukata.

Ismail Ibrahim Dutse ya kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Malam Dr. Umar A. Namadi bisa goyon baya da tallafin da ta bayar domin gudanar da wannan shiri ga mambobin kungiyar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version