kungiyar ‘Yan Jarida ta NUJ a Jigawa ta tsige shugaban Correspondents Chapel saboda shiga siyasa
Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa ta sanar da tsige shugaban kungiyar Correspondents Chapel, Kwamared Zangina Mohammed Kura, daga mukaminsa nan take bayan ficewarsa daga aikin jarida da kuma shiga takarar siyasa a zaben shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da majalisar kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an dauki matakin ne bayan korafe-korafe da kuma sahihan bayanai da suka tabbatar da cewa Kwamared Zangina Mohammed Kura ya daina aikin jarida tare da tsayawa takarar kujerar dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Kura/Garin Malam karkashin jam’iyyar ADC a zaben 2027.
Sanarwar ta ce matakin ya yi daidai da kundin tsarin mulkin kungiyar NUJ, musamman sashe na 5, 7 da 8, wadanda suka shafi da’a ta aikin jarida, ladabtarwa da hukunci kan duk wani abu da zai bata martabar kungiyar.
Kungiyar ta bayyana cewa shiga harkokin siyasa na bangaranci da jami’in kungiyar ke yi yana tauye martaba, gaskiya da kuma kwarewar aikin jarida, wanda hakan ya saba wa ka’idojin aikin jarida.
Haka kuma, kungiyar ta ce bisa kudurorin da majalisar zartarwa ta kasa (NEC) ta amince da su, duk wani dan kungiyar da ya shiga siyasa ko ya karbi mukamin siyasa dole ne ya sauka daga mukaminsa na kungiyar domin kare martabar kungiyar a matsayin mai zaman kanta.
Saboda haka, kungiyar ta umarci Kwamared Zangina Mohammed Kura da ya mika dukkan wasu nauyin aiki, takardu da kadarorin kungiyar ga mataimakin shugaba ba tare da bata lokaci ba, har sai an bayar da wasu umarni na gaba.
Sanarwar ta yi gargadin cewa duk wani kin bin wannan umarni zai sa a mika lamarinsa ga kwamitin ladabtarwa da da’a na kungiyar domin daukar mataki kamar yadda kundin tsarin mulkin NUJ ya tanada.
Kazalika, kungiyar ta bukaci ma’aikatu, hukumomi, kungiyoyin farar hula, jami’an tsaro da sauran jama’a su daina mu’amala da Zangina Mohammed Kura a matsayin shugaban Correspondents Chapel.
A karshe, kungiyar NUJ reshen jihar Jigawa ta sake jaddada kudirinta na kare kwarewa, da’a, rashin nuna bangaranci da kuma bin kundin tsarin mulkin kungiyar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version