Filin wasannin na Sani Abacha, na Gwamnatin Tarayya ne, ba mallakin mutum guda bane dukkanin Dan Jihar kano, yana Alfahari da shi domin FC BARAU DA KANO PILLARS, duk na mutanen kano ne.

Karkasara yace abin Alfahari ne ace Ansamu kungiyoyin Kwallon Kafa masu karfi, guda biyu a Jihar kano, Kamar yadda kowa yaaani cewar Jihar kano tayi shura a fagen wasannin motsa jiki,kana Rana guda ace wani ya hura iska ya bugi kirji ya hana kungiyar Kwallon Kafa, ta Barau FC buga wasa a filin wasa na Sani Abacha,wannan ba Dai – dai bane.
Duk da dai Gwamnatin ta yi amai ta lashe, sakamakon umarnin data samu daga Asalin masu filin wasa na sani Abacha wato gwamnatin tarayya, domin Gwamnatin Jihar kano tana mantawa da lamba 5 na kasa take so tayi rigima.
Barau FC kungiyar Kwallon Kafa ce data ke kan mataki na daya a gasar rukunin Kwallon Kafa ta kasa, Haka zalika, kano pillars.

