Tuni dai shirye – shirye sunyi nisa, na bikin cikar kwalejin Rumfa shekaru 100 da kafuwa.
Yayin da karamin kwamitin Yada Labarai karkashin Dr, Goni faruk Umar, ya fara zama domin gudanar da shirye – shiryen da suka kamata
DR, GONI FAROUK SHUGABAN KWAMITIN YADA LABARAI
Daga cikin abubuwan da kwamitin ya kunsa Akwai, Babban kundi do za, ayi Mai dauke da fitattun mutanen da suka yi makarantar da suka hada da sarakuna da Shugabannin kasa.
Sakataren karamin kwamitin Yada Labarai Dr Adamu sa, ad Madaki yayi Karin haske akan wannan kwamitin, ya bayyana cewar wannan kwamitin yana da matukar mahimmanci bisa yadda aka zabo mahimman mutane da zasu baje basirar su wajen fitar da tarihin makarantar da gudunmawar da aka baiwa makarantar Ada da yanzu, kana za, a baiwa wasu da dama lambobin yabo, bisa irin Agajin da suke baiwa makaranta Akwai wasan Kwallon Kafa da gabatar da mukala da tarurruka karawa juna Sani, do ziyarce – ziyarce, harda uwa Uba Gwamnan Jihar kano da sauran masu madafun iko da zasu taimaka akai ga nasara, da gabatar da shirye – shirye a kafafen Yada Labarai domin Karawa bikin Armashi.
Tuni dai kwamitocin da aka kafa sun fara aiki karkashin Ajiyan kazaure Alh Nu, uman Barau Danbatta.

