Malam Baba madatai shine yajagoranci Matasan darikar Tijjaniyya ta kasa Reshen Jihar kano yayin da suka Kai ziyarar ta ya murna ga sabon shugaban gidan Radio Guarantee 94.7 FM dake Jihar kano Alh Abubakar Balarabe Kofar Naisa.
Malam madatai ya bayyana cewar nadin da aka yiwa Alh Abubakar ya dace bisa la, akari da irin kwarewarsa wajen aikin jarida da Kuma yadda yasaba baiwa Addinin musulinci gudnmawa ta kowacce fuska,tare da yin Kira ya rungumi kowa – da kowa Dan kaiwa ga Nasarar da aka sa agaba
Amadadin yayan kungiyar na kasa Malam Baba Madatai sun Taya murna tare da fatan Alheri ga sabon shugaban gidan Radio na guarantee.
