MAI MARTABA SARKIN BAUCHI YA JA HANKALIN SHUGABANNI SU GUJI ZALUNCI SU KAMANTA GASKIYA
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Maimartaba Sarkin Bauchi Alhaji Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu ya shawarci shugabanni su kasançe masu nuna jagoranci na gaskiya tare da nisantar da kawunan su daga aikata miyagun ayyuka, don su samu gamuwa da Allah lafiya.
Sarkin ya bayyana haka ne cikin jawabinsa a wajen taron bita kan nuna jagoranci na gaskiya a cikin al’umma, wanda kungiyar Muslim Ummah reshen jihar Bauchi ta shirya a dakin taro na sansanin alhazai da ke Bauchi.
Babban limamin masallacin Jumaah na fadar maimartaba Sarkin Bauchi Alhaji Bala Ahmed Baban Inna, shine ya wakilci Sarkin a wajen taron.
Yadda ya bayyana cewa maimartaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya bukaci shugabanni su sani Allah madaukakin sarki ya yi umarni da adalci da kyautatawa, Kuma Manzo SAW. bai yarda a zalunci kowa ba, hatta wanda ba musulmi ba ya bukaci musulmi ya ba shi hakkin sa a kowane yanayi Idan mu’amala ta hada su.
Don haka addinin musulunci ya gargadi musulmi ya nisanci taka hakkin musulmi da wanda ba musulmi ba, saboda adalci shine tubalin ginin al’umma ta gari. Kuma ya zamo wajibi dukkan shugaba ya kamanta adalci lokacin da yake jagoranci.
Daga karshe Sarkin na Bauchi ya yi fatar kowane shugaba ya sauke nauyin da aka dora masa bil hakki da gaskiya don ya samu gamuwa da Allah lafiya.
Haka kuma ya yi fatar kungiyar Muslim Ummah da sauran kungiyoyin da suke aiki tare, za su ci gaba da shirya irin wannan taron don farkar da mutane daga barci saboda da a samu gyaruwar lamurran shugabanci da zamantakewa a cikin al’umma.

