Kakakin hukumar kashe gobara ta Kano ya rasu

Allah ya yi wa kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, CFO Saminu Yusuf Abdullahi, rasuwa.

Shugaban shiyyar hukumar ta Dambatta, PFS2 Muhammad Ibrahim Nasiru, ne ya tabbatar da rasuwar ga Premier Radio.

Marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a tare da isar da bayanai kan ayyukan hukumar, musamman abubuwan da suka shafi kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

An gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar Laraba, 7 ga Oktoba 2026, a Jihar Kano.

Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannar Firdausi ce makomarsa. Amin.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version