MAJALISAR DOKOKIN KANO TA AMINCE DA NAƊIN MURTALA SULE GARO A MATSAYIN MATAIMAKIN GWAMNA

Majalisar Dokokin Jihar Kano (KNHA) ta amince tare da tabbatar da naɗin Hon. Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar.
Mataimakin Kakakin Majalisar kuma Shugaban Kwamitin Tantancewa, Rt. Hon. Muhammad Bello Butu Butu, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan gabatar da rahoton kwamitin a zauren majalisar, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jubril Ismail Falgore.
Ya ce kwamitin ya ba da shawarar amincewa da naɗin ne bayan ya tabbatar da cewa wanda aka naɗa ya cika dukkan ka’idojin da aka gindaya wa kwamitin, waɗanda suka haɗa da duba shekarunsa, takardun karatu, asalinsa a jihar, ƙwarewar aiki da kuma kasancewarsa cikakken ɗan jam’iyya mai katin shaida.
Shugaban kwamitin ya ƙara da cewa binciken ya nuna cewa Murtala Sule Garo ya haura mafi ƙarancin shekaru 25 da ake buƙata, ɗan asalin ƙaramar hukumar Kabo ne, yana da takardar Higher National Diploma (HND), kuma cikakken mamba ne na jam’iyyar APC.
Haka kuma ya bayyana cewa Garo na da ƙwarewa a fannin siyasa da gudanarwa, kasancewarsa tsohon shugaban ƙaramar hukuma, tsohon shugaban ƙungiyar ALGON, kwamishina, tare da kasancewarsa ɗan takarar mataimakin gwamna a baya.
Daga ƙarshe, ya taya shi murnar samun wannan amincewa tare da miƙa godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon baya da haɗin kai da ya bai wa majalisar.

Yanzu haka dai ana jiran ranar da za, a rantsar da shi

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version