Kasancewar sa kusa acikin jam, iyyar Apc a kasa Nijeriya da Jihar kano, tsohon kwamishinan kudi zamanin Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, Dr, mukhtar Dan Amu ya bukaci masu hannu da shuni da su tallafawa masu karamin karfi kasancewar zuwan watan Azumin Ramadan.
Dr mukhtar Dan Amu na wannan bayaninne a meenah event center dake kano a Yayinda yake baiwa marayu da malamai da masu, unguwanni Kayayyakin Abinci domin Shirin tarbar Azumin watan Ramadan.
Hon Dan, Amu ya ce Shima maraya ne Akwai bukatar masu hali su kaiwa marayu da makwabta dauki.
Tun da farko jawabin sa shugaban jam, iyyar Apc na Jihar kano Alh Abdullahi Abbas ya Ja hankalin yayan jam, iyyar Apc na Jihar kano da wadanda ke rike da mukamai a Gwamnatin Tarayya da su kawo dauki domin Akwai bukatar AL, ummar musulmi suyi Azumi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Da yake jawabi jagoran jam, iyyar Apc tsohon shugaban ta na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Yabawa Dr Aminu mukhtar Dan, amu tare da yin kira ga AL, umma da suyi koyi dashi bisa irin tagomashin da yayi wa marayu da sauran mabukata.

Tun da farko Sai da wakilin Gwamnan Jihar kano kwamared Ibrahim Waiya ya bayyana cewar wannan na daya daga cikin manufofin gwamnatin Alh Abba Kabir Yusuf.
Dattijo Alh Hamza Darma da kwamishina Yada Labarai na Jihar kano kwamared Ibrahim Waiya da tsohon mataimakin shugaban majalisar Dokokin Jihar kano, Alh Aliko Shu, aibu da shugaban hukumar raya kogunan hadejia da jama Alh Rabiu suleiman Bichi da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar kano Alh Baffa Bichi da, malamai da masu unguwanni da marayu Maza da Mata da matasa daga mazabu 13 na karamar hukumar Birni.
