Your message has been sent
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma mai neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin ba zai janye daga neman takarar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, wadda mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya sanya wa hannu.
