Gwamnan Kano ya kori ɗan gidan Kwankwaso daga kujerarsa ta kwamishinan matasa da wasanni.

Wasu rahotanni da bamu gama tabbatar da sahihancinsu ba sun bayyana cewar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin ɗage zaman majalisar zartarwa zuwa karfe 1:15 na yau Laraba bayan hallarar kwamshinoninsa inda ya sallami goma daga cikinsu harda ɗan ɗan Sanata Kwankwaso.

Da farko an tsara gudanar da zaman da karfe 11 na safe kafin a ɗage, a ƴan kwanakin nan, an yi ta yaɗa jita-jitar cewa gwamnan zai sanar da da komawarsa jam’iyyar APC a zaman majalisar zartarwa da zai jagorata a ranar Laraba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version