Kamar yadda yasaba baiwa Al, ummar jihar Kano romon Dimukradiyya Sanata Barau I Jibrin Yayinda ya fara da kano ta Arewa,, yayin da kowace karamar hukuma mutane Dari biyar ne suka Amfana da kudi Naira dubu 20 Ashirin yanzu Kuma a gudanar da kano ta tsakiya yayin da matasa da Mata zasu
Haka zalika nan bada Dadewaba za, a bada irin wannan tallafin kudin ga AL, ummar yankin kano ta kudu, domin su Amfana Kana. a Kwai tallafin karatu ga Dalibai kimanin dubu 4,ne suka Amfana da tallafin karatu masu karatun Degree naira dubu 50 yayin da masu karatun NCE zasu Amfana da kudi Naira dubu 20., Wanda ake gudanar wa duk shekara domin karawa Dalibai karfin gwiwa, yanzu haka Sanata Barau I Jibrin, zai baiwa dukkan Daliban da ke karatu a manyan makarantun Jihar kano.
Kamar yadda kwamared Adamu Abdullahi karkasara ya (SLA) Mai taimakawa mataimakin shugaban majalisar Dattawa na kasa Sanata Barau I Jibrin ya bayyana cewar yanzu haka Akwai Ayyukan da ake gudanar na sanya fitilu masu Amfani da hasken Rana a yankin kano ta Arewa.
Adamu Abdullahi karkasara ya Kara da cewar, DSP Barau I Jibrin nan bada dadewa ba Sanatan zai bada tallafin kekunan dinki da Injinan markade, dubu daya da Dari uku da injinan mirjin taliya guda dubu 1 da Dari uku da fulawar taliya guda dubu 1 da Dari uku omin bunkasa tattalin arziki ga AL, ummar Jihar kano.,dake yankin kano ta Arewa.
Haka zalika matasa Yan Kwallon Kafa, da ake sa ran Kowacce karamar hukumar zata kawo kungiyar Kwallon kafa guda 150, da Sanata Barau I Jibrin ya bayar da umarnin Kowacce karamar hukuma kungiyar Kwallon kafa zasu Amfana da Kayayyakin wasanni da suka hada da Kwallon Kafa da taguwar Kwallon Kafa da takalma da sauransu.
