Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta nuna damuwa kan matakin da hukumomin Saudiyya suka ɗauka na rage wa Najeriya yawan kujerun aikin Hajji da aka ware mata. Hukumar ta ce wannan mataki zai hana dubban ‘yan Najeriya damar gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta bayyana cewa Saudiyya ta keɓe wa Najeriya kujeru 66,910 kacal – wanda ya haɗa da kujerun jihohi 51,513, na jami’an hukumar, da kuma 15,397 na kamfanonin tafiye-tafiye.
NAHCON ta ce an rage kujerun ne saboda Najeriya ta kasa cikewa gaba ɗaya kujerun 95,000 da aka ware a shekarar 2025, inda aka bar sama da 35,000 babu masu cikawa. Wasu ‘yan Najeriya sun danganta hakan da tsadar kuɗin aikin Hajjin bara wanda ya sa mutane da dama suka kasa halarta.

