Wani shahararren mai daukar hoto da yashafe shekaru 30 yana wannan sana,ar ya ce yanzu zamani yazo harkar hoto na neman zama,Tarihi sakamakon zuwan wayoyin hannu da sabuwar fasahar AI,wadda ana iya cewa babbar barazana ce ga harkar.

Malam Muhammad Idris (BANKWALE MAI HOTO) yace,shekarun baya akwai farin hoto (Black & White) Wanda shima zamani yayi awon gaba dashi,da a baya zaka iya ajiye hoto na Tarihi mai hade da Yan, uwa da Abokan Arziki.

 

Zuwan wayar hannu ta sanya ba, a daukar hoto kamar shekarun baya da mai hoto ya zama tamkar dan lele ko ana iya cewa sarki a fagen, saboda motsi kadan,a kirashi yayi abinda ya dace.

BANKWALE MAI HOTO yace sana, ar hoto tayi masa sutura domin kuwa dukkan rufin Asirin ALLAH yayi masa ta wannan fuskar,kuma ya koyar da matasan wannan zamani sana,r hoton,gashi har ya samu lambar girmamawa dake nuni da cewar shima ya taka rawa a fannin cigaban jihar kano.

 

Sanar, ar hoto sana,ace dake nuni cewar tana da babban kalubale tsakanin ta da sabuwar fasahar AI,fasahar AI dake sauya fasali da kamannin mutum.

A shekarun baya ana ajiye tarihi na hoto,sabanin yanzu da ake dauka a wayar hannu,idan ta samu matsala shi kenan an rasashi ko mai kyawunsa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version