RUNDUNAR YAN SANDAN BAUCHI TA BA NDLEA SINKIN WIWI 378 DA AKA SAMU CIKIN MOTAR DA TA YI KARO DA MOTAR HAKIMIN NABORDO
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi CP Sani Omolarin Aliyu ya hannata kunshin tabar wiwi 387 da suka cafke a cikin wata Mota da ta yi hatsari kan hanyar Bauchi zuwa Jos a ranar 4/10/2025.
Sani Omolarin ya mika buhunnan a lokacin taron manema labarai da ya kira a ofishin sa a safiyar juma’a 10/12025.
Bayan kammala jawabinsa cikin harshen turanci kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi CSP Mohammed Ahmed Wakil ya yi karin bayani da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike don gano direba da wanda suka mallaki tabar wiwi guda 387 a cikin mota da ta yi hatsarin saboda tuni suka tsere.
Rundunar ta ce hatsarin ya faru a ranar 4 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:30 na safe a ƙauyen Wom dake ƙaramar hukumar Toro, a Jihar Bauchi, wanda ya kunshi motoci biyu kirar Toyota Corolla.
Binciken farko ya nuna cewa motar farko, Toyota Corolla fara mai lamba ABC-459LF, mallakin Ali Muhammad, mai shekara 45 daga ƙauyen Nabardo, tana ɗauke da Hakimin Nabardo, Alhaji Suleiman Bala Suleiman mai shekara 65 da iyalansa, suna kan hanyarsu daga Bauchi zuwa Nabardo.
Mota ta biyu, Toyota Corolla mai lamba GWA-155GW, wadda direbanta da ba a kai ga gano asalinsa ba, tana tafiya ne daga Jos Jihar Filato, zuwa Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa direban ya yi yunƙurin wuce wata mota ne ba tare da kula ba, hakan ya jawo taho mu gama da motar farko.
Dukkan fasinjojin motoci biyun sun samu raunuka iri-iri, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin kula da lafiyar su, inda aka tabbatar Hakimin Nabardo ya samu karaya a kafa, yayin da wasu daga cikin fasinjoji suka samu sauƙi kuma aka sallame su.
Cikin bincike a wajen hatsarin, jami’ai sun gano abubuwa da dama a cikin motar mai kirar Toyota Corolla (GWA-155GW) da ta lalace, ciki har da: busasshiya tabar wiwi kulli 387 da sauran kayayyaki.
An miƙa kayan da aka gano ga sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike, kafin daga baya aka miƙa lamarin ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.
Rundunar tana ci gaba da neman direban motar domin gano mai kayan don a gurfanar da shi a gaban kotu. Haka kuma Kwamishinan ya roƙi duk wanda ke da bayanai game da shi ya sanar da jami’an tsaro.
Mataimakin Kwamandan NDLEA a Bauchi Malam Hussain Umar ya godewa rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi game da taimakon da suka yi wajen cafke wannan kaya. Don haka ya bayyana cewa za su ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Hussain Umar ya bukaci Jama’a su ci gaba da taimaka musu don samun nasarar gudanar da aikin su a jihar Bauchi.
