MAI MARTABA ALHAJI MUSA AHMAD ABBA, SARKIN SUDAN GAYA, YA NAƊA SABBIN MASU SARAUTA

          A wani biki mai cike da ɗaukaka da martaba, Mai Martaba Alhaji Musa Ahmad Abba, Sarkin Sudan Gaya, ya gudanar da bikin naɗa sabbin masu sarauta a ranar Alhamis, 30 ga Yuli, 2026, domin ƙarfafa tsarin masarauta da bunƙasa hidima ga al’umma.
Muƙaman da aka naɗa sun haɗa da:
Fulanin Sarkin Sudan Gaya
Wakilin Sarkin Sudan Gaya
Chiroman Sarkin Sudan Gaya
Sarauniyar Sarkin Sudan Gaya
A jawabinsa, Mai Martaba Alhaji Musa Ahmad Abba ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗe  bisa cancanta cancanta, riƙon amana da kyakkyawan ɗabi’a. Ya buƙaci sabbin masu sarautar su kasance masu adalci, tawali’u, haɗin kai da hidima ga al’umma domin ci gaban masarautar da ƙasa baki ɗaya.
Bikin ya samu halartar manyan baƙi, masu sarauta, malamai, shugabannin al’umma waɗanda suka taya sabbin masu sarautar murna tare da yi musu addu’ar Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da aka ɗora musu.
An kammala taron cikin farin ciki da addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba ga Masarautar Sarkin Sudan Gaya da Jihar Kano baki ɗaya.
Allah Ya ƙara wa Mai Martaba Alhaji Musa Ahmad Abba lafiya, tsawon rai da ɗaukakar masarauta, Ya kuma ba sabbin wadanda aka nada a masarautar sarautar nasarar gudanar da rikon amanar da aka basu ,musu. Amin

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version