Babban shafin tallata tafiyar Kwankwasiyya karkashin Jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Facebook wato Kwankwasiyya Reporters ta sanar da sauya sunan shafinsa zuwa Gida Gida Reporters, a wani mataki da ya ce an ɗauka domin ƙarfafa rawar da shafin yake takawa wajen wayar da kan al’ummar Jihar Kano kan harkokin mulki da ayyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
A cewar sanarwar da wakilin shafin Muhammad M. Alasan, ya fitar ga manema labarai na gidan Gwamnatin Kano, sauyin sunan na da nufin mayar da hankali kan yaɗa bayanai da rahotanni game da tsare-tsare, da manufofi da ayyuka masu amfani ga jama’a da gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf.
TST Hausa ta rawaito cewa an kirkiri shafin ne tun a shekarar 2016 domin tallata akidar tafiyar tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso karkashin Jagorancin shugaban karamar hukumar Kumbotso Ghali Basaf.
Shafin na Kwankwasiyya Reporters da aka Sauyawa suna yana da mabiya dubu 720 a yanzu haka tun bayan samar da shi.
Sanarwar ta kuma yi tsokaci kan rade-radin cewa an sauyawa shafin suna ne domin juyawa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso baya, Yayinda suke kallonsa amatsayin uba.
Muhammad ya kuma shaidawa TST Hausa cewa sun mika batun sauya sunan, ga hukumomin Facebook inda suke jiran amincewa, domin cigaba da tallata Ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf.
