Tsohon ministan tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya karyata labarin da ake yadawa a kafafan sada zumunta cewa yana cikin tattaunawa domin sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu tsohon gwamnan jihar Jigawa kana tsohon ministan tsaro Badaru ya jaddada labarin baida tushe balle makama, kuma wani yunkuri ne na yaudara a siyasa.

Kazalika ya kara da cewa yana nan daram cikin jam’iyyar APC wacce ya taimaka aka kafa, kuma biyayyarsa ga jam’iyyar ba ta da wata tangarda.

Ya bukaci jama’a da mambobin jam’iyyar APC da su yi watsi da irin waɗannan rahotannin na ƙarya da ruɗu, yana mai jaddada cewa yana nan tsaye a matsayin ɗan jam’iyyar APC mai jajircewa, kuma babu wani shiri ko niyyar barin jam’iyyar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version