Matashin ya koka bisa yadda yace Gwamnan jiha ya baiwa kungiyar JUBWIS kimanin Naira malala, Amma gashi masu fama da cutar koda na fuskantar matsaloli babu iyaka musanman ma,yadda,tun kafin wannan lokacin suna kira ga Gwamnan jihar da yayi wa Allah da manzansa,ya kai dauki domin gina cibiyar masu kula da ciwon koda.

Bayan da matashin yaji shiru ne,sai yashiga kafar sada zumunta,yayi kira ga Gwamnan jihar bisa yadda Gwamnan yobe ya yi wannan aikin Baban giwa.

Yanzu dai zamu jira mugani Gwamnan jihar yobe mai mala zai Amsa kira ko kuwa zai cigbaa da yin Biris da masu wannan cutar da ko zai kai daukin gaggawa.??

Sau dayawa shugabanni suna kulawa da sashin lafiya tare da bashi mahimmanci ,haka kuma a kasashen da suka cigaba,ana baiwa Ilimi da harkar lafiya mahimmanci.

Jaridar muryar Arewa A yau.com    ta tuntubi mai baiwa Gwamnan jihar yobe shwara.  Shariff Almuhajir,muna jira da zarar ya bamu amsa zamu sanar wa duniya domin jin ta bangaren Gwamnan jihar yobe.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version