Dan Takarar ADC Ya Karɓi Fom Din Tsayawa Takara Don Majalisar Dattawan Kano ta Kudu a Zaɓen 2027

Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Zulyadaini Sidi Mustapha, ya bayyana cewa ya karɓi fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara daga hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja domin neman kujerar Sanatan Kano ta Kudu a babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Zulyadaini ya ce matakin ya biyo bayan tattaunawa mai faɗi da masu ruwa da tsaki, magoya baya da kuma mambobin jam’iyyar.
Ya kuma bayyana cewa bayan tantancewa da jam’iyyar ta gudanar, an amince da shi tare da ayyana shi a matsayin ɗan takara guda tilo na maslaha da jam’iyyar ADC za ta tsayar domin fafatawar.
Dan takarar ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka ba wai fito-na-fito ba ne da kowa ko kuma sakamakon saɓani na kashin kai, yana mai cewa yana mutunta Sanatan da ke kan kujerar tare da kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu.
Ya ce dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar samar da zaɓuɓɓuka masu kyau, sababbin tunani da kuma tattaunawa mai amfani domin cigaban al’umma baki ɗaya.
Zulyadaini ya bayyana cewa dalilin tsayawarsa takara shi ne domin inganta wakilci, ƙarfafa muradin al’ummar Kano ta Kudu da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban yankin.
Ya yi alƙawarin samar da wakilci mai ma’ana da ya ta’allaka kan adalci, haɗin kai, bai wa matasa dama, ilimi, bunƙasa tattalin arziki da ci gaban rayuwar jama’a.
Haka kuma ya buƙaci al’ummar Kano ta Kudu da su haɗa kai domin tabbatar da samar da yankin da ya fi ƙarfi da wadata ga al’ummomin yanzu da masu zuwa.
A ƙarshe, ya roƙi Allah da Ya ba su jagoranci tare da albarkaci Kano ta Kudu baki ɗaya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version