A yayin da al’umar Musulmi ke shirye shiryen fara azumin Ramadan Sarkin Kano Bayero ya mika bukata ga “Yan kasuwa.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci “Yan Kasuwa su saukakawa al’uma a lokacin watan Ramadan.
Alhaji Aminu Ado Bayero Ya bukaci hakan ne lokacin da yake kaddamar da kungiyar Daliban Masarautar Kano wanda aka gudanar a fadar Sarkin dake Nassarawa a Birnin Kano.
Sarkin yace a irin wannan lokaci da al’umar Musulmi ke shirye shiryen fara gabatar da azumin watan Ramadan na wannan shekara akwai bukatar ‘yan Kasuwa ako ina suyi sauki a kayayyakinsu ga al’umar Musulmi domin su sami damar siyayyar kayan masarufi da sauran kayan da zasuyi amfani dasu a cikin watan Ramadan da kuma sauran lokuta.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’uma su zage damtse wajan gabatar da ibada tareda kasancewa cikin tsarkakakkiyar zuciya dayin addu’oi domin samun zaman lafiya da karuwar arziki da gyaruwar tattalin arziki da kuma masana’antu.
Yayi kira ga Malamai su cigaba da fadakar da al’uma wajan kaucewa barna da gyaran halaye da kyautatawa juna.
Daga nan Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’ar Allah ya cigaba dayi mana maganin dukkan abubuwan da suke damun al’umar Musulmi tarteda kawo sauki cikin al’amuran rayuwa.
