Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), sakamakon rikice-rikicen cikin gida da ke kara kamari a jam’iyyar, tare da bukatar kare muradun al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.
A cikin wasikar da ya kaiwa Shugaban NNPP na Ward din Diso-Chiranchi, Karamar Hukumar Gwale,
Gwamna Yusuf ya bayyana a hukumance cewa ya janye daga jam’iyyar tun daga Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.
“Ina rubuto wannan wasika ne cike da godiya domin sanar da shugabancin jam’iyyar NNPP hukuncin da na dauka na ficewa daga jam’iyyar, wanda zai fara aiki daga Juma’a, 23 ga Janairu, 2026.”
Gwamnan ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da goyon bayan da ya samu tun lokacin da ya shiga NNPP.
“Ina matukar godiya ga jam’iyyar, shugabanninta da mambobinta a fadin Jihar Kano bisa damar da suka ba ni tun shekarar 2022, da kuma goyon baya, fahimta da hadin kai da na samu a lokacin da nake cikin jam’iyyar.”
Ya bayyana cewa rikice-rikicen shugabanci da shari’o’i da ke gudana a kotuna sun girgiza tubalan jam’iyyar a matakin kasa baki daya.
“A baya-bayan nan, jam’iyyar ta fada cikin rikice-rikice masu yawa na cikin gida, sakamakon sabanin shugabanci da kuma shari’o’i da dama da ke gaban kotuna.”
A cewarsa, wadannan sabani sun haddasa rarrabuwar kai mai tsanani a cikin jam’iyyar.
“Rashin jin dadi da ke kara yaduwa tsakanin mambobin jam’iyyar ya haifar da babbar baraka, wadda ke kara raunana hadin kai tare da jefa jam’iyyar cikin rashin tabbas a matakin jiha da kasa.”
Gwamna Yusuf ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan dogon nazari, bisa la’akari da muradun jama’a kawai.
“Bayan yin nazari mai zurfi, na yanke shawarar cewa ficewata daga jam’iyyar ita ce mafi alheri ga al’ummar Jihar Kano.”
Ya kara da cewa ya dauki matakin ne cikin lumana, ba tare da gaba ko kiyayya ba.
“Na dauki wannan hukunci cikin kyakkyawar niyya, ba tare da wata gaba ba, tare da ci gaba da jajircewa wajen samar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Jihar Kano.”
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan ya fice daga NNPP tare da ‘yan Majalisar Jiha 21, ‘yan Majalisar Wakilai 8, da Shugabannin Kananan Hukumomi 44 na Jihar Kano.
Sakataren jam’iyyar NNPP na Ward din Diso-Chiranchi, Hon. Kabiru Zubairu, ya tabbatar da karbar wasikar ficewar, inda ya yabawa gwamnan bisa manyan ayyukansa a bangarorin more rayuwa, gyaran birane, lafiya, ilimi da karfafa tattalin arziki.
“Na amince da maganar Mai Girma Gwamna kan rikicin da ya dade yana addabar jam’iyyar. Duk da kokarin da muke yi na shawo kansa, ba mu da wani zabi illa karbar ficewar daya daga cikin gwamnonin NNPP mafi kwazo da aiki.”
