Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen jihar Kano, ta ayyana ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2026, a matsayin ranar gudanar da zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano a ƙananan hukumomin Ungoggo da Kano Municipal.
INEC ta ce za a gudanar da zaɓen ne domin cike guraben kujerun majalisar da suka samu babu kowa, sakamakon rasuwar ‘yan majalisar dokokin jihar guda biyu da ke wakiltar waɗannan yankuna a baya-bayan nan.
Hukumar ta buƙaci dukkan jam’iyyun siyasa da su hanzarta miƙa sunayen ‘yan takararsu, tare da tabbatar da cewa sun cika dukkan ƙa’idoji da sharuɗɗan da dokar zaɓe ta tanada.
INEC ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki na daga cikin nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata, domin tabbatar da cikakken wakilci ga al’ummar jihar Kano a Majalisar Dokoki.
Hukumar ta kuma jaddada ƙudirinta na gudanar da sahihin zaɓe mai inganci, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki jam’iyyu, hukumomin tsaro da al’umma baki ɗaya da su bayar da haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a lokacin gudanar da zaɓen.
