Sanarwar ta bayyana cewa ya dauki matakin ne bayan zurfin tunani da tuntuba tare da bayyana yakini kan damar da ke gaban al’ummar Kano ta Tsakiya, musamman matasa da mata a matsayin ginshikin ci gaban al’umma.

 

Usman Bala yace  kudiri aniyar bunkasa rayuwar al’umma ta hanyar samar da damammaki ga matasa da tallafawa mata da kuma inganta shugabanci, inda ya nemi goyon baya da addu’a daga jama’a domin cimma burinsa.

 

Kujerar Sanatan Kano ta tsakiya dai na ci gaba da samun farin jini kasancewar wanda ya ke kai Sanata Rufaʼi Sani Hanga yana jamʼiyyar adawa.

 

Daga cikin fitattun masu neman kujerar akwai Hon. Abdussalam Abdulkarim AA Zaura wanda ya yi wa APC takara a 2023, kuma ɗaya daga cikin ƴan tsohuwar APC mafi kusanci da Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf.

 

Rahotonnin  sun nuna cewa , a cikin mazawartan kujerar akwai tsohon Sanatan yankin wato Sanata Bashir Garba Lado wanda a yanzu shi ne hadimin Shugaban Kasa kan Harkokin Majalisar Dattijai.

 

Sai kuma Tsohon Dan Majalisar Tarayya na Birni da Kewaye kuma Hadimin Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wato Malam Shaʼaban Ibrahim Sharaɗa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version