Wata sanarwa da kafar Yada Labarai ta Murray Arewa Ayau ta fitar ta bayyana jagoran Yan dangwale na gidan marigayi Sanata Isah Yahya zarewa, Hon Khalid Ahmad Zarewa (Tsohon kirki)tsohon kansila Mai gafaka, kuma tsohon Dantakarar majalisar jiha daga yankin karamar hukumar Rogo yayi Bankwana da tsohuwar jam, iyyar NNPP kana ya tsunduma acikin jam, iyyar Apc Kamar yadda Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf ya yi.
Duk masanin Tarihi yasan yadda Khalid yayi takarar Sanata a yankin Kano ta kudu A jam’iyar ADP 2023.
Tsohon dantakar chairman na karamar hukumar rogo A Jam’iyar NNPP 2024.
Khalid Ahmad yace “” A madadina da magoya baya. da sakomakon tattaunawa da mukayi ,munsami mafi rinjayen kuri’un magoya bayanmu cewar mun amince da umarnin da jagororinmu na karamar hukumar mu ta rogo mai albarka suka bamu cewar muyi mu baya’a a ga mai girma zababben gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf mai lakabi da Abba gida gida,Abban kanawa.
Hon Khalid yace yana amfani da wannan dama nasanar da dukkannin Al’Umar karamar hukumar rogo, da Kano ta kudu da Al, ummar jihar Kano da Nigeria cewar daga laraba 28/1/2026 munfice daka jam’iyar nnpp kuma munshiga jam’Iyar APC.
Bisa girmamawa munayiwa kowa da kowa fatan Alkhairi Ayi siyasa bada gaba ba domin taken mu shine siyasarmu Addininmu Addininmu siyasarmu.
Hon Khalid Ahmad ya yi kowa fatan Alheri da fatan samun Nasara a rayuwa tare da yiwa kowa fatan Alheri musanman Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf.
Tare da yin Addu, a ga marigayi Sanata Isah Yahya zarewa da dukkan magabatan mu.
