RT Hon Alhassan Ado Doguwa Sardaunan kasar hausa Mai tuta OON ya bayyana rasuwar Alkali ALh Hamza Usman Darma,da cewar Babban rashine,ga kasa baki daya bisa la,akari da mu,amulla da kyakykyawan manufofi da Dabiu da Dattako da yake dashi.
Doguwa Wanda mai magana da yawun sa Auwal Ali Sufi utai SLA,ya wallafa a shafinsa yace rasuwar Alkali ALh Hamza Usman Darma,ya girgiza shi, alokacin da ya samu labarin rasuwarsa.
Hon Alhassan Ado ya mika sakon ta, aziyya ga Sarkin kano da Gwamnan jihar kano da Yan, uwa da magoya,bisa rasuwar Alkali ALh Hamza Usman Darma
Rt Hon Alhassan Ado Doguwa yayi Addu,ar ALLAH yajikansa Allah ya hada kan iyalansa
