An bai wa Waiya lambar yabon ne domin karrama rawar da yake takawa wajen tafiyar da harkokin sadarwa a lokutan rikici da kuma isar da sahihan bayanai kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati ga al’umma.
Shugaban Image Merchants Promotions Limited, *Farfesa Sule Ya’u Sule*, ya ce an zaɓi Waiya ne bayan tantancewa bisa ƙoƙarinsa na isar da sahihan bayanai cikin lokaci da kuma bin ƙa’idojin aikin sadarwa.
Da yake karɓar lambar yabon, Kwamared Waiya ya sadaukar da ita ga Gwamnan Jihar Kano, *Alhaji Abba Kabir Yusuf*, da ma’aikatan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, da kuma kafafen yaɗa labarai na jihar.
Kwamishinan ya jaddada muhimmancin isar da sahihan bayanai cikin lokaci wajen tabbatar da shugabanci nagari, yana mai tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da ƙarfafa sadarwa tsakanin gwamnati da al’ummar Jihar Kano.
