Adai-dai lokacin da masana sharhi irin na siyasa suka hangi wasu alamomi dake nuni da haske ko akasin hakan,zakaga yadda,akan yiwa masu ruwa da tsaki hannunka mai sanda domin agyara ko daukar matakin da yadace, ko a kwanannan anga yadda, mataimakin Gwamnan jihar kano Hon murtala sule Garo yayi dogon zama da jiga -jigan jam, iyyar APC na kiru da Bebeji,wato majidadin kiru da Hon Abdul Maumee jibrin kofa, Danmajalisar wakilan na Tarayyar,domin samo bakin zaren dan kaiwa ga Nasara a Babban zabe mai zuwa.
Haka abin yake a wasu wuraren,na yankin mazabar kano ta kudu dake da, sanata suleman Abdur Rahman kawu sumaila ofr Marafan Rano, Wanda a kwanannan ya baje mahimman Ayyukan raya kasa da ya gudanar a gaban daruruwan matasa da Jama,ar yankin kano ta kudu,Har Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ya shaida hakan domin shima ya bada gudunmawa.da,kauren kano ta kudu shugaban Yan majalisun Arewacin nijeriya rt Hon Alhassan Ado Doguwa Sardaunan kasar hausa Mai tuta OON , Wanda kana iya ce masa limamin siyasar da ke haske fitilar tsira ga Wanda ya bishi
Duk da kasancewarsa farin wata sha kallo a siyasa,bai sa ya kaucewa umarnin Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ba hasalima dai aikin Gandu yakewa tafiyar shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu da Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf domin kaiwa ga Nasara,
Kwatsam kuma sai akajiyo wasu maganganu na tashi a yankin karamar hukumar Tudun wada,da suka kara karfafawa jam, iyyar APC gwiwa na shugabar karamar hukumar Hajiya Sa,adatu yusha u soja (ALGON), wadda tasha Aradun cewar jam, iyyar APC zata kai ga Nasara a Babban zabe mai zuwa,ma,ana tun daga kan sanata na kano ta kudu, zuwa Danmajalisar wakilan na Tarayyar Nijeriya,zuwa zaben gwamna jihar kano da Danmajalisar Dokokin jihar kano.,
yayinda a gefe guda ake so aga hadin kai yacigaba tsakanin kansilolin da aka ware suma a basu tagomashin Dimukradiyya,kamar yadda aka baiwa takwarorinsu domin a tafi baidaya.wannan zai karawa tafiyar dankon zumunci da Nasarar da ake bukata,fatan Hajiya zata duba
Shugabar Ƙaramar Hukumar Tudun Wada kuma Shugabar ALGON ta Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja, ta bayyana goyon bayanta ga Hon. Alhassan Ado Doguwa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauye a harkokin siyasar yankin Doguwa da Tudun Wada.
