KUNGIYAR TSOFFIN SHUGABANNIN KANANAN HUKUMOMI NA JIHAR KANO SUN SHA ALWASHIN MARAWA GWAMNAN JIHAR KANO BAYA DON
Adai-dai lokacin da Babban zabe ke karatowa, yayinda jam, yyun ke baza haja da neman goyan baya na mutanen Birni da karkara,,sako da lungu, domin neman hadin kai dan kaiwa ga Nasara,sai ga kungiyar Tsoffin Shugabannin ƙananan hukumomin na jihar kano, wadanda suka yi mulki A shekarar 1997/98,zamanin Tsohon shugaban kasa Muhammad Sani Abacha Suka taru da a gidan Mumbayya Karkashin jagorancin Kwamishinan yada labarai na jihar kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya,Domin nuna goyan baya da kuma Amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf yayi Hawa na biyu a Babban zabe mai zuwa domin cigaba da mahimman Ayyukan raya kasa Ajihar kano.
Wannan batu ya sa ma,ajin kungiyar Kuma Tsohon shugaban karamar hukumar Doguwa Hon Kabir Abdullahi Riririwai y, Wanda ya ke bayani a madadin shugaban kungiyar na jihar kano Hon Nazir Zakari sheka Tsohon shugaban karamar hukumar kumbotso yake kara jaddada aniyar wannan kungiyar na baiwa Gwamnan jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf Tabbacin cewar zasu yi aiki Tukuru,domin ganin Ansamu Nasara a Babban zabe mai zuwa,

Hon Kabir Abdullahi Riririwai yace jihar kano tana bukatar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cigaba da Ayyukan raya kasa da Tausaywa Al’umma ta kowacce fuska,samarda Hanyoyi,gine -gine bunkasa noma da kiwo da bada Ilimi,da sauran su babu shakka jihar kano zata cigaba da mortar Romon Dimukradiyya
Riririwai yace tuni suka kaddamar da kungiyar karkashin jagorancin Kwamishinan yada labarai na jihar kano Kwamared Ibrahim Abdullahi waiya,Harma suka sa ka mata suna TUNUBU/ABBA GRASS ROOT MOBILISATION ASSOCIATION.