Alkali Hussaini Ahmadu Sufi, ya rasu a safiyar yau Alhamis a gidansa da ke unguwar Charanci a cikin birnin Kano.

Marigayi Alkali Hussaini Sufi ya yi fice wajen kafa makarantu na Islamiyya da suka taimaka wajen koyar da Alƙur’ani da ilimin addini ga dubban dalibai.

Haka kuma ya taka muhimmiyar rawa a harkar da’awa, musamman wa’azin Maguzawa, inda kokarinsa ya taimaka wajen jawo mutane da dama zuwa addinin Musulunci.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version