Ƴansanda sun kama mutane 2 bisa zargin hannu a kisan Ibrahim Khalil Ɗanshagamu a Kano

Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan Ibrahim Khalil Danshagamu, mazaunin unguwar Gaida, karamar hukumar Kumbotso.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, 8 ga Satumba 2026, bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kutsa gidan marigayin tare da kai masa hari da wukake.

Rundunar ’yansandan ta ce kwamandan kungiyar Vigilante ta Gaida ne ya sanar da ita lamarin, inda jami’an sashen ’yan sanda na Kumbotso suka garzaya wurin.

An garzaya da Danshagamu zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano domin ba shi agajin gaggawa, amma likita ya tabbatar da rasuwarsa bayan isar sa asibitin.

Kakakin rundunar ’yansandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke wadanda ake zargin ne bayan wani samame na leken asiri da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarni.

Ya ce jami’an sashen Kumbotso, tare da hadin gwiwar rundunonin dabarun aiki da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, ne suka gudanar da samamen.

A halin yanzu, wadanda ake zargin na hannun ’yansanda kuma ana yi musu tambayoyi, yayin da ake kokarin cafke wasu da ka iya kasancewa da hannu a lamarin.

Rundunar ta ce ana karbar bayanan wadanda abin ya shafa, tare da gudanar da binciken kimiyyar laifuka domin gano cikakken bayani da kuma dalilin harin.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version