Bayan an kai ruwa rana, jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Birni ta kammala zaɓen sabbin shugabanninta.

A jawabin da Baturen zaben, Hon. Muhammad Shehu, ya yi, an bayyana Hon. Munzali Abubakar Dambazau a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

Siyasarmu TV ta rawaito, taron ya samu halartar Baffa Babba Ɗan’Agundi, Muntari Ishaq Yakasai, Shugaban ƙaramar hukumar Birni Hon. Salim Hashim, zaɓaɓɓen ɗan majalisar jiha Hon. Nabil Sarki Aliyu Daneji da wasu shugabanni, amma ba a ga fuskar Sagir Ƙoƙi wanda shine wakilin yankin a tarayya ba.

Sai dai rahotanni sun nuna Sagir Ƙoƙi ya bayyana rashin amincewarsa da sakamakon zaɓen, inda ya fice daga taron, yana mai cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi masa alkawarin shugabancin jam’iyyar.

Wannan lamari na iya haifar da sabani tsakanin jagororin jam’iyyar a ƙaramar hukumar Birni yayin da ake ci gaba da bibiyar yadda za a warware rikicin.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version