Kamar yadda yasaba tsarge gaskiya a dukkan lokacin da hakan ta taso shugaban Yan majalisun Arewacin Nijeriya Rt Hon Alhassan Ado Doguwa, yayi jirwaye da Kamar wanka game da zaben shekara ta 2027 dake zuwa.
“Duk wanda yake tunanin wannan zaben mai zuwa babu matsala to bai shirya taimakon Gwamna da jam’iyyar APC ba, dan haka mu mun shirya kuma muna kiran kowa ya zama dan takara domin tunkarar 2027”
Doguwa na wannan batunne a gidan Gwamnatin Jihar kano, yayin taron masu ruwa da tsaki na na jam, iyyar Apc Shiyyar kano ta kudu,
~ Hon. Alhassan Ado Doguwa, yayi nuni ga gwamnatin jiha data yi duk Mai yiwuwa wajen shirya tsare – tsaren da zasu baiwa AL, umma damar Gwamnan Jihar kano Alh Abba Kabir Yusuf ya sake zama gwamna a Karo na biyu domin cigaban Jihar kano da AL, ummar kano baki daya.
A wani jawabi da wakilin Tudunwada da Doguwa ya yi a wajan taron da Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci gudanar da shi a yau.
Ya bayyana cewa “idan al’umma sun manta ya kamata su tuna domin a zaɓen 2023 ina gidan yari na samu nasara a TudunWada da Doguwa”
