DG na NPC, Dan Agundi, Ya Jinjinawa Ziyarar Gwamna Abba Kabir Yusuf Zuwa Rundunar ’Yan Sanda, Ya Ce Haɗin Gwiwa Ne Mabuɗin Kawar da Laifuka a Kano
Daraktan Janar na Cibiyar Ƙara Ƙwazo ta Ƙasa (National Productivity Centre – NPC), Dr. Baffa Babba Dan’agundi, NIM, ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ziyarar aiki da ya kai Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano da ke Bompai. Ziyarar ta zo ne domin yabawa Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, kan ƙwarewa da jajircewar da rundunar ta nuna wajen kama waɗanda ake zargi da kisan gilla na wata mata da ’ya’yanta shida a Ciranchi, Karamar Hukumar Kumbotso.
Dr. Dan’agundi ya bayyana ziyarar Gwamnan a matsayin abin ƙara wa jami’an ’yan sanda ƙwarin gwiwa, inda ya ce irin wannan ziyara na ƙarfafa su su ƙara himma wajen sauke nauyin da ke kansu. A cewarsa, “Irin wannan ziyara daga Gwamna za ta ƙara wa ’yan sanda kwarin guiwa su ƙara zage damtse, ganin cewa ana gane sadaukarwarsu da ƙwarewarsu tare da yaba musu a matakin jagoranci mafi girma.”
Ya ƙara da cewa jagorancin CP Bakori ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro a Jihar Kano, yana mai jaddada cewa tasirin aikinsa a fili yake a faɗin jihar. Dr. Dan’agundi ya nuna cewa tun bayan karɓar muƙamin Kwamishinan ’Yan Sanda, an samu gagarumin ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya da rage aikata laifuka a birane da karkara.
Da yake yabawa salon jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Dr. Dan’agundi ya bayyana shi a matsayin shugaba mai tawali’u kuma mai sauraron jama’a. Ya ce, “Gwamna shugaba ne mai sauraro, wanda ke daraja ra’ayoyin al’umma tare da karɓar shawarwari masu amfani. Ziyararsa zuwa Hedikwatar ’Yan Sanda ba alama kawai ba ce, illa tabbatacciyar shaida ta shugabanci nagari.”
Dr. Dan’agundi ya jaddada cewa ziyarar ta nuna muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin tsaro. Ya ce ci gaba da wannan haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da rundunar ’yan sanda shi ne hanya mafi inganci wajen kawar da aikata laifuka tare da tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano. Ya ƙara da cewa alkawarin da Gwamnan ya yi na ci gaba da aiki kafada da kafada da CP Bakori mataki ne mai kyau na cimma Kano mai aminci da tsaro.
