Akalla ƴan majalisar wakilai guda takwas daga Jihar Kano sun sanar da sauya sheƙarsu daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC, a zauren majalisar wakilai ta tarayya da ke Abuja.

Wani makusanci ga tsohon gwamnan Kano Ganduje ya shaidawa tashar Dan’uwa Rano TV cewa, ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da:

Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe, mai wakiltar Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa

Hon. Garba Ibrahim Diso, mai wakiltar Gwale

Hon. Hassan Shehu Hussain, mai wakiltar Nassarawa

Hon. Idris Dankawu, mai wakiltar Kumbotso

Hon. Muhammad Chiroma Nalaraba, mai wakiltar Gezawa/Gabasawa

Hon. Barrister Rabiu Yusuf, mai wakiltar Takai/Sumaila

Hon. Dr. Ghali Mustapha Tijjani, mai wakiltar Albasu/Gaya/Ajingi

Hon. Barrister Muhammad Bello Shehu, mai wakiltar Fagge.

Rahotanni sun nuna cewa sauya sheƙar tasu ta gudana ne a hukumance a gaban sauran ƴan majalisa, inda suka bayyana dalilansu na komawa jam’iyyar APC.

An rawaito cewa manyan jiga-jigan siyasa sun halarci wannan taro, ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, tare da sauran shugabannin jam’iyya.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa wannan sauya sheƙa na iya kawo gagarumin sauyi a tasirin jam’iyyun siyasa a Jihar Kano, musamman a matakin majalisar tarayya.

 

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version