Kungiyoyin matasa da ke Yada Addinin musulinci, na cigaba Neman Tallafi Domin Gudanar da Shirin Da’awah na MPD a Jihar Kaduna
Yayinda a gefe guda.  Liktoci Muslim, kwararru, dake da kwarewa a fanni daban – daban da malamai masu Yada Addinin musulinci Da’awah Sun sauka a ihar Kaduna

 

ta bayyana shirinta na gudanar da wani babban shirin wa’azi (Da’awah) a karamar hukumar Kubau daga ranar Juma’a 3 ga Afrilu zuwa Lahadi 5 ga Afrilu, 2026.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce shirin na da nufin karfafa zaman lafiya tsakanin al’umma, inganta tarbiyya, yada addinin Musulunci da kuma tallafa wa al’umma musamman masu bukata. Haka kuma, an bayyana cewa shirin zai kunshi ayyukan jinkai da kuma bada kulawar lafiya ga al’ummomin da ke cikin bukata.
Kungiyar ta kara da cewa irin wannan shiri da ta gudanar a baya a jihohin Bauchi  da Gombe ya yinda ya samu nasarori masu yawa. Daga cikin nasarorin da aka samu akwai mutane 777 a Lausuba, 725 a Miya, 206 a Dulayala, 23 a Toro (duk a Bauchi), da kuma 74 a Bambam (Gombe) da suka amfana da shirin.
Kungiyar ta ce wadannan nasarori sun kara musu kwarin gwiwa wajen fadada ayyukansu, tare da ci gaba da ilmantar da wadanda suka karbi addinin Musulunci domin su fahimci addinin yadda ya kamata.
A karshe, kungiyar ta yi kira ga jama’a da su bada gudummawa domin tallafa wa wannan shiri, tana mai cewa kowace irin gudummawa, babba ko karama, za ta taimaka wajen rage nauyin da ke kanta, kuma za ta zamo sadaka mai dorewa (Sadaqatul-Jariya) ga mai bayarwa.
Kungiyar ta gode tare da fatan samun hadin kai daga al’umma

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version