A makon nan, siyasar Najeriya ta shiga ruɗani bayan wani labari mai yaduwa kamar wutar daji ya bayyana cewa tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya fice daga APC zuwa jam’iyyar ADC domin shirye-shiryen zaɓen 2027.
Labarin ya bazu sosai a kafafen sada zumunta, ya jawo muhawara mai zafi tsakanin ‘yan siyasa, masu sharhi, da magoya bayan jam’iyyun siyasa a faɗin ƙasar. Amma tambayar ita ce: shin gaskiya ne ko kuwa jita-jitar siyasa ce?
A ranar 8 ga Janairu, 2026, wasu shafukan labarai na intanet sun wallafa rahoto da ke cewa Abdullahi Adamu ya bar APC ya koma ADC. Rahoton ya ce an tarbe shi a wani taro a Keffi, Jihar Nasarawa, inda ake cewa shugabannin ADC sun yi murnar shigowarsa jam’iyyar.
Wannan labari ya yi ƙarfi a WhatsApp, Facebook da X (Twitter), inda mutane da dama suka ɗauka a matsayin gaskiya — musamman ganin yadda ake ta samun sauya sheƙa-sheƙa a siyasar Najeriya gabanin 2027.
Sai dai, sa’o’i kaɗan bayan labarin ya bazu, manyan hujjoji suka fara bayyana da ke karyata zancen:
• Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta fitar da sanarwa inda ta ce labarin ƙarya ne tsagwaronta, tana mai jaddada cewa Abdullahi Adamu har yanzu cikakken memba ne na APC.
• Abdullahi Adamu da kansa ya yi magana da manema labarai, inda ya ce labarin ƙirƙira ne kuma neman suna kawai. Ya bayyana cewa bai da niyyar barin APC, yana mai cewa:
“Ba ni da hali na zama ɗan siyasar da ba ya godiya.”
• Wani rahoto kuma ya nuna cewa Adamu ya sabunta katin APC ɗinsa a rumfar zaɓensa da ke Keffi, abin da ya ƙara ƙarfafa cewa ba a samu wata ficewa daga jam’iyya ba.
Binciken da ZANCEN YAU ya hudanar, ya nuna cewa wannan ruɗani bai zo haka nan ba:
🔹 Yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, ana samun sauya sheƙa-sheƙa da yawa daga manyan ‘yan siyasa, wanda ke sa jama’a su yi saurin yarda da duk wani labari makamancin haka.
🔹 Wasu hotuna da bidiyo na baya an sake amfani da su ba tare da sahihancin bayani ba, aka nuna su a matsayin hujjar sauya sheƙa.
🔹 A siyasar zamani, labarin da bai tabbata ba kan fi yaɗuwa fiye da gyaransa, musamman a kafafen sada zumunta.
4. Tasirin Wannan Jita-jita ga APC da Siyasar 2027
Yayin da Najeriya ke tunkarar zaɓen 2027, irin waɗannan labarai za su ƙaru. Amma gaskiya ɗaya ce, wacce ZANCEN YAU ya gano: Abdullahi Adamu bai bar APC ba
Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version