GWAMNA NAMADI YA YABA WA SHUGABA TINUBU KAN SHIRIN RANCIN KARATU GA DALIBA
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙaddamar da Asusun bada lamuni na Ilimi na Ƙasa (NELFUND), inda ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki da ya zo a kan lokacin da ake bukatar sa domin rage radadi bisa kuɗin karatu da ke kan dalibai a faɗin ƙasar nan.
Gwamnan ya yi wannan yabo ne a ranar Talata,   yayin da yake karɓar baƙuncin mambobin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na Ƙungiyar Dalibai Najeriya (NANS), ƙarƙashin jagorancin Shugaban  ƙungiyar, Kwamared Olusola Ladoja, a ziyarar ban-girma da suka kai masa a Fadar Gwamnati da ke Dutse. Jihar jigawa 

Shugabannin NANS sun kasance a Jihar Jigawa ne domin gudanar da zaɓen shiyyar Arewa maso Yamma na ƙungiyar, wanda ya haɗa da jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa, Sokoto da Kebbi.
Gwamna Namadi ya nuna godiya bisa zaɓen Jihar Jigawa a matsayin mai masaukin baki, tare da tabbatar da aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da tallafa wa ayyukan NANS da duk wasu shirye-shiryen da suka shafi walwalar dalibai.
Da yake jawabi kan shirin baiwa Dalibai, bashi.           gwamnan ya ce wannan tsari na nuna ƙwarin gwiwar Shugaba Tinubu wajen bunƙasa ilimi da kula da jin daɗin dalibai.
Ya tuna da irin ƙalubalen da dalibai ke fuskanta sakamakon ƙarin kuɗin makaranta, inda ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ta zuba jari mai yawa domin tallafa wa dalibai marasa ƙarfi a matsayin wani ɓangare na shirinta na bunƙasa jarin bil’adama.
“Ina iya tuna lokacin da aka ƙara kuɗin makaranta, dalibai da dama sun samu matsala wajen biya. A gaskiya ma, wasu sun kusa barin makaranta, wanda ba abin yarda ba ne.         Gwamnatin Jihar Jigawa, ta hannun ofishin kula da harkokin dalibai, ta yi aiki tukuru wajen biyan kusan naira miliyan ɗari bakwai domin taimaka wa dalibanmu su biya kuɗin makaranta.
“Don haka, shirin bada bashi ga dalibai da Shugaba Tinubu ya ƙaddamar ya nuna mana cewa wannan shugaba ne mai kishin ilimin matasa a Najeriya.”da San cigaban Ilimi.

Gwamna Namadi ya kuma yaba wa shugabancin NANS bisa ƙarfafa tattaunawa, haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin dalibai, tare da jan hankalinsu da su rungumi gaskiya, riƙon amana da shugabanci nagari, kasancewarsu shugabannin gobe.

 


“Kuma ina farin ciki da ganin cewa Shugaban kungiyar Dalibai NANS da dukkan shugabannin sun fahimci cewa tattaunawa, sadarwa da fahimtar juna su ne mafita. A matsayinmu na shugabannin gobe, akwai buƙatar mu warware sabaninmu ta hanyar zama a teburin tattaunawa, ba ta rikici ba.”
A nasa jawabin, Shugaban kungiyar Dalibai na NANS, Kwamared Olusola Ladoja, ya yaba wa gwamnatocin tarayya da jihohi bisa manufofinsu na kula da dalibai, inda ya bayyana shirin rancen dalibai a matsayin wani gagarumin sauyi da ke nuna sabon salo na shugabanci mai sauraron ƙorafin dalibai tare da daukar mataki a kansu.
“Tun bayan kafuwar dimokuraɗiyya a wannan ƙasa, wannan ne karo na farko da daliban Najeriya ke jin daɗin kyakkyawar alaƙa da shugaban ƙasa. Wannan ne shugaban ƙasa na farko da ke sauraron daliban Najeriya. Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne shugaban ƙasa na farko da ya ga dacewar bai wa daliban Najeriya rance domin su samu damar yin karatu.”
Shugabannin NANS sun kuma nuna godiya ga Gwamnatin Jihar Jigawa bisa samar da yanayi mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda ya ba da damar gudanar da zaɓen shiyyar Arewa maso Yamma cikin nasara, tare da jaddada aniyarsu ta ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version