wani bangare na ƙoƙarin gwamnatinsa na faɗaɗa samar da gidaje masu nagarta da araha a faɗin Jigawa State, Gwamna Malam Umar Namadi ya kaddamar da sabon mataki na ayyukan gidaje ƙarƙashin Hukumar Gidaje ta Jihar.
An gudanar da bikin ne a ranar Alhamis a birnin Dutse, hedikwatar jihar, inda kuma aka ƙaddamar da shirin horas da sana’o’in hannu ga matasa 135 da aka zabo daga ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya tuna cewa kimanin shekaru biyu da suka gabata ne aka fara shirin gidaje na jihar, inda ya ce an samu gagarumin ci gaba zuwa yanzu.
“Da dama daga cikinmu za su tuna cewa kusan shekaru biyu da suka gabata, a ranar Asabar 20 ga Janairu, 2024, muka gudanar da bikin aza harsashin ginin mataki na farko na shirin gidajenmu a wurare daban-daban a fadin Jihar Jigawa. Zuwa yau, an kammala kusan gidaje 1,050 daga cikin 1,500 da aka tsara, kuma za a ƙaddamar da mataki na uku a wannan shekara, in sha Allah,” in ji shi.
Gwamnan ya bayyana sabon shirin a matsayin wani tsari na musamman da nufin sake fasalta da inganta Hukumar Gidaje ta Jihar Jigawa domin ta zama hukuma mai cin gashin kanta ta fuskar kuɗi, wadda za ta iya sauke nauyin samar da gidaje masu nagarta da araha ga ma’aikatan gwamnati da sauran al’umma.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samar da asusun zuba jari na naira biliyan 2 domin bai wa Hukumar Gidaje damar fara aiwatar da shirin, yana mai nuna kwarin gwiwa cewa ƙarfafa hukumar zai taimaka wajen hanzarta samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Gwamna Namadi ya jaddada cewa shirin ya yi daidai da buri na 9 cikin ajandar gwamnatinsa mai maki 12, wadda ta mayar da hankali kan bunƙasa ababen more rayuwa na birane, gyaran birane da kuma faɗaɗa ayyukan gidaje masu araha.
Ya yabawa Ma’aikatar Filaye da Hukumar Gidaje ta Jihar bisa kokarinsu, yana mai cewa aza harsashin ginin gidaje 52 masu dakuna biyu da uku a Dutse ya buɗe sabon babi ga hukumar.
“Domin cimma wannan buri, dole ne Hukumar Gidaje ta tafiyar da asusun zuba jarin cikin gaskiya da ƙwarewa, tare da mai da hankali kan hanzarta samar da gidaje masu araha da tabbatar da kyakkyawan riba kan jarin da aka zuba,” in ji gwamnan.
Haka kuma ya buƙaci hukumar ta nemi haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu tare da amfani da sabbin fasahohi da za su rage kuɗin gini da sauƙaƙa mallakar gida ga jama

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version