Gwamna Namadi Ya Sanya Hannu Kan Tsarin Ayyukan OGP Na Uku, Ya Umarci Ma’aikatu Su Bai Wa Gaskiya Da Riƙon Amana Muhimmanci
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, bai wa al’umma damar shiga cikin harkokin gwamnati da kuma inganta shugabanci nagari, yayin da ya sanya hannu a hukumance kan Tsarin Ayyukan Open Government Partnership (OGP) na Jihar Jigawa na Uku (2026–2027).
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Dutse, bayan da Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa kuma Shugaban Kwamitin Jagorancin OGP na jihar, Injiniya Aminu Usman, ya gabatar masa da rahoto kan sakamakon taron kwanaki biyu na tantancewa da amincewa da sabon Tsarin Ayyukan.
Gwamna Namadi ya kuma umarci dukkan Ma’aikatu, Hukumomi da Sassan Gwamnati (MDAs) da su bai wa aiwatar da wannan shiri muhimmanci matuƙa, yana mai jaddada cewa nasarar aiwatar da shi za ta ƙara inganta shugabanci nagari, ƙarfafa amincewar jama’a ga gwamnati da kuma bunƙasa isar da ingantattun ayyuka ga al’umma.
Rahoton da aka gabatar ya nuna cewa an tantance tare da amincewa da Tsarin Ayyukan ne bayan wani tsari na haɗin gwiwa da ya haɗa da hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, abokan hulɗar ci gaba, kamfanoni masu zaman kansu da kuma jama’a.
Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa an tsara hanyoyin aiwatar da shirin tare da daidaita shi da Ajandar Gwamnatin Namadi mai Muhimman Batutuwa 12 domin tabbatar da nasarar aiwatar da manufofin.
Gwamna Namadi ya yabawa Mataimakin Gwamnan, Kwamitin Jagorancin OGP na jihar, shugabannin gwamnati da na ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, Sakatariyar OGP, ƙungiyoyin fararen hula, abokan hulɗar ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai wajen samar da wannan muhimmin kundin manufofi.
Ya ce:
“Na yi matuƙar farin ciki da karɓar Tsarin Ayyukan Open Government Partnership (OGP) na Uku na Jihar Jigawa (2026–2027), wanda ke nuna haɗin kanmu wajen ƙarfafa shugabanci na buɗaɗɗe a jihar.”
A cewarsa, wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, bai wa jama’a damar shiga harkokin gwamnati da kuma inganta ayyukan gwamnati domin biyan buƙatun al’umma.
Gwamnan ya ƙara da cewa sanya hannu kan wannan kundin na nuni da cewa buɗaɗɗen shugabanci da riƙon amana su ne ginshiƙan tafiyar gwamnatinsa.
“Da sanya hannu kan wannan takarda a yau, muna sake tabbatar da cewa buɗaɗɗen shugabanci ba buri kawai ba ne, illa jagorar tafiyar wannan gwamnati. Don haka na yi alƙawarin tabbatar da cikakken aiwatar da wannan Tsarin Ayyukan.”
Ya kuma umarci dukkan Ma’aikatu da Hukumomin da ke da alhakin aiwatar da abubuwan da ke cikin wannan shiri da su haɗa su cikin shirye-shiryensu na yau da kullum domin tabbatar da cikakken aiwatarwa.
Hakazalika, ya yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula, abokan hulɗar ci gaba, kamfanoni masu zaman kansu, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, mata, matasa da masu buƙata ta musamman da su ci gaba da haɗa kai da gwamnati har zuwa ƙarshen aiwatar da shirin.
Tun da farko, Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman, ya yi wa Majalisar Zartarwa ta Jiha bayani kan sakamakon taron tantancewa da aka gudanar a Kaduna daga ranar 31 ga Yuli zuwa 1 ga Agusta, 2026, inda mahalarta taron suka duba, suka tantance tare da amincewa da Tsarin Ayyukan OGP na Uku.
Ya ce taron ya kuma samar da taswirar aiwatar da shirin domin fara aiki nan take tare da tabbatar da cewa ya yi daidai da manufofin ci gaban jihar.
Rahoton ya bayyana cewa Tsarin Ayyukan ya ta’allaka ne kan manyan manufofi guda huɗu da suka haɗa da:
- Inganta gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.
- Sauƙaƙa samun adalci ga jama’a.
- Ɗaukar matakan kare muhalli da sauyin yanayi.
- Yaƙi da cin hanci da rashawa tare da bayyana kadarorin jami’an gwamnati.
Masu ruwa da tsaki sun kuma amince cewa dukkan Ma’aikatu da Hukumomin da za su aiwatar da shirin su haɗa waɗannan manufofi cikin shirye-shiryensu na shekara-shekara, kasafin kuɗi da ayyukansu, yayin da gwamnati da abokan hulɗar ci gaba za su haɗa kai wajen samar da kuɗaɗe da sa ido kan yadda ake aiwatar da shirin.
A ƙarshe, sanarwar taron ta sake jaddada kudurin Jihar Jigawa na ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi buɗaɗɗen shugabanci, tana mai bayyana cewa aiwatar da Tsarin Ayyukan OGP na Uku (SAP III) zai ƙara inganta gaskiya, riƙon amana, shigar jama’a cikin harkokin gwamnati, inganta isar da ayyuka da kuma tallafa wa ci gaba mai ɗorewa a Jihar Jigawa.
