A wani sabon mataki da ke ƙara nuna tsanantar rikicin da ke tsakanin hamshaƙin attajirin Najeriya kuma mamallakin kamfanin mai na Oriental Energy Resources, Muhammadu Indimi, da tagwayen ‘ya’yansa mata, attajirin ya bayyana cewa zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya umarce shi da ya biya su dala miliyan 43.51 sakamakon takaddamar da ta shafi rabon riba.

Wata majiyar kuma daga shafin jaridar Daily trust ta rawaito cewar INDIMI YA NEMI SHIGA ƘARAR DAUKAKA KARA KAN HUKUNCIN BIYAN ’YA’YANSA MATA DALA MILIYAN 43.5
Attajirin ɗan kasuwar man fetur na Najeriya kuma wanda ya kafa kamfanin Oriental Energy Resources, Alhaji Muhammadu Indimi, ya nemi izinin shiga cikin ƙarar ɗaukaka kara kan hukuncin kotu da ya umarci kamfanin ya biya tagwayen ’ya’yansa mata dala miliyan 43.51 saboda rikicin da ya shafi haƙƙinsu na rabon ribar hannun jari.
Buƙatar ta zo ne a wani sabon salo da shari’ar ta ɗauka, lamarin da ya jawo muhawara daga masana da masu ruwa da tsaki kan batutuwan haƙƙin masu hannun jari da kuma tsarin gadon kamfanonin iyali masu zaman kansu a nahiyar Afirka.
Tagwayen ’ya’yan Indimi da ke shigar da ƙarar su ne Zara Indimi da Ameena Indimi.
Buƙatar da Muhammadu Indimi ya gabatar ta biyo bayan ɗaukaka ƙarar da kamfanin Oriental Energy Resources ya shigar tun da farko, bayan Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci a watan Fabrairu na goyon bayan Ameena da Zara Indimi.
A cikin ƙarar tasu, tagwayen sun yi zargin cewa an hana su haƙƙinsu na rabon ribar kamfani bayan an rage yawan hannun jarin da suke mallaka a kamfanin, lamarin da suka ce ya tauye musu haƙƙinsu.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version