Gwamna Namadi: Mun Dukufa Wajen Bunƙasa Wasanni Daga Matakin Ƙasa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na bunƙasa harkokin wasanni tun daga matakin ƙasa domin gano hazaka, ƙarfafa matasa, da kuma inganta haɗin kai a faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin babban wasan ƙarshe na gasar ƙwallon ƙafa tsakanin unguwannin Ƙaramar Hukumar Hadejia, wanda aka gudanar a filin wasa na Hadejia Township Stadium.
Gasar ta haɗa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daga dukkan unguwanni goma sha ɗaya na Ƙaramar Hukumar Hadejia, kuma Akanta Janar na Jihar Jigawa, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ne ya ɗauki nauyin shirya ta.
A wasan ƙarshe, ƙungiyar GRA Ward ta zama zakara bayan ta doke Sabon Garu Ward tare da lashe kofin gasar.
Gwamna Namadi ya bayyana wannan gasa a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaban wasanni a Ƙaramar Hukumar Hadejia, inda ya yabawa Akanta Janar bisa ɗaukar nauyin shirin da ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta bunƙasa wasanni.
Ya ce:
“Ina tabbatar wa duk wanda ya shiga wannan gasa, tun daga wasan farko har zuwa na ƙarshe, cewa dukku kun yi nasara. Wannan shiri ya yi daidai da manufar gwamnatinmu ta bunƙasa harkokin wasanni da kuma bai wa matasanmu damar bayyana cikakkiyar baiwar da Allah Ya ba su ta hanyar wasanni.”
Gwamnan ya tuna cewa daga cikin umarnin farko da gwamnatinsa ta bayar bayan hawanta mulki akwai umurtar Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu da ta samar da ingantaccen tsarin bunƙasa wasanni daga matakin unguwanni, zuwa ƙananan hukumomi, sannan a ƙare da gasar jiha baki ɗaya.
A cewarsa, shirin ya fara haifar da kyakkyawan sakamako, inda aka samar da ƙungiyar Jigawa Junior Golden Stars, wadda yanzu ke fafatawa a gasar Nigeria Nationwide League One (Division Two), kuma dukkan ‘yan wasan ƙungiyar ‘yan asalin Jihar Jigawa ne.
Ya ƙara da cewa:
“Wannan shi ne abin da muka sanya a gaba tun farko, kuma cikin ikon Allah mun cimma hakan. Za mu ci gaba da aiwatar da irin wannan tsari a sauran fannoni na wasanni domin ƙara bunƙasa harkar wasanni tare da bai wa matasa damar bunƙasa baiwarsu tun daga tushe.”
Har ila yau, Gwamna Namadi ya sanar da cewa ya umarci Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu da ya tabbatar an gyara tare da inganta filin wasan Hadejia Township Stadium cikin watanni shida masu zuwa domin samar wa matasan yankin ingantattun wuraren wasanni.
Gwamnan ya kuma miƙa godiyarsa ga mai ɗaukar nauyin gasar, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, da Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, ƙungiyoyin da suka halarci gasar, alkalan wasa, da sauran masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudummawa wajen samun nasarar shirya gasar.
Tun da farko, Akanta Janar na Jihar Jigawa, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ya bayyana cewa an shirya gasar ne domin ƙarfafa haɗin kan matasa ta hanyar wasanni, tare da samar da wata dama ta gano da kuma bunƙasa hazikan ‘yan wasa tun daga matakin ƙasa.
Ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa bai wa ci gaban matasa da wasanni muhimmanci, yana mai cewa manufar bunƙasa wasanni daga tushe da gwamnatin ta bullo da ita za ta taimaka wajen gano zakarun gobe tare da ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar.
