Jihar Jigawa Na Samun Gagarumin Ci Gaba a Muhimman Bangarori — Gwamna Namadi
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa jihar na ci gaba da samun gagarumin ci gaba a muhimman bangarori sakamakon zuba jari da gyare-gyaren da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron Dandalin Ci Gaban Yankin Jigawa ta Arewa maso Gabas da aka gudanar a Kaduna karkashin jagorancin Majalisar Masarautar Hadejia.
Gwamna Namadi ya yaba wa masu shirya taron bisa samar da dandali domin tattauna kalubalen ci gaban da yankin ke fuskanta.
Ya ce, “Batutuwan da aka gabatar hakikanin matsaloli ne da ke bukatar kulawa ta musamman. Abin farin ciki shi ne ba wai gano matsalolin kadai aka yi ba, har ma an gabatar da hanyoyin magance su. Wannan kansa ci gaba ne.”
Gwamnan ya bayyana cewa duk da wasu alkaluman tattalin arziki da aka gabatar na nuna tsoffin matsaloli, jihar na ci gaba da samun sauyi mai kyau sakamakon shirye-shiryen gwamnati.
“Wasu daga cikin alkaluman da aka gabatar na iya nuna halin da ake ciki a baya, amma ina tabbatar muku cewa da dama daga cikin wadannan matsaloli suna raguwa saboda zuba jarin da muka yi a muhimman bangarori,” in ji shi.
Dangane da karuwar yawan jama’a da bunkasa jarin dan Adam, Gwamna Namadi ya ce gwamnatinsa na kokarin mayar da yawan jama’ar jihar wata dama mai anfani.
“Eh, karuwar jama’a kalubale ne, amma idan aka sarrafa ta yadda ya dace za ta zama wata babbar dama. A Jigawa mun kuduri aniyar mayar da jama’armu jarin dan Adam mai anfani.”
A bangaren samar da wutar lantarki kuwa, gwamnan ya bayyana yadda aikin samar da hasken rana da aka fara a Kafin Hausa ya zama babban ginshiki wajen bunkasa harkokin kasuwanci a yankin.

“A yau al’ummomin yankin suna samun kusan awa 24 na wutar lantarki. Fiye da haka ma, abin burgewa shi ne yadda kananan sana’o’i suka bunkasa sakamakon wannan aiki. Harkokin tattalin arziki sun fadada sosai,” in ji shi.
Gwamna Namadi ya kara da cewa nasarar wannan aikin ta sa gwamnatin jihar ta kara zuba jari a bangaren makamashi mai sabuntawa, ta hanyar kafa masana’antar hada kayayyakin hasken rana a jihar domin tallafa wa aikin samar da megawatt 100 na lantarki.
Ya ce za a raba wutar lantarkin tsakanin yankunan sanatoci uku na jihar, inda Jigawa ta Arewa maso Yamma za ta samu megawatt 40, yayin da Jigawa ta Arewa maso Gabas da Jigawa ta Tsakiya za su samu megawatt 30 kowacce.
Ya bayyana cewa an ware kaso mafi yawa ga yankin Arewa maso Yamma ne saboda akwai yankin sarrafa kayayyakin fitarwa na Maigatari da kuma cibiyar masana’antu ta Jigawa da ke Gagarawa.
“Tattaunawa ta kai mataki mai zurfi kuma ana sa ran fara aikin nan ba da jimawa ba. Kayayyakin hasken rana da za a yi amfani da su za a samar da su ne a Jigawa,” in ji gwamnan.
A bangaren noma kuwa, Gwamna Namadi ya ce gwamnatin jihar ta shiga hadin gwiwa da kamfanoni hudu daga kasar Indiya a fannoni daban-daban na harkar noma da suka hada da samar da iri, kiwo, kiwon kaji da kasuwancin noma.
“Daya daga cikin muhimman bangarorin shi ne samar da iri. Mun gudanar da gwaje-gwaje masu nasara a cibiyoyin bincikenmu ta amfani da ingantattun irin daga Indiya kan masara, shinkafa da alkama da sauransu.”
Ya ce irin masarar da aka gwada sun bayar da tan 10 a kowace hekta idan aka kwatanta da tan biyu ko uku da ake samu daga irin gida.
Haka kuma ya ce irin shinkafar sun yi kyau sosai, inda wasu suka bayar da tan shida, bakwai da rabi har ma da tan takwas a kowace hekta karkashin yanayin jihar Jigawa.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnati na amfani da bunkasa kiwo a matsayin hanyar rage rikice-rikicen manoma da makiyaya tare da inganta rayuwar jama’a.
“Idan muka yi nasara da wannan tsari, ba kawai za mu kara kudaden shiga na makiyaya da manoma ba, har ma zai taimaka sosai wajen rage rikice-rikice tsakanin al’umma,” in ji shi.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar na mayar da hankali wajen kara darajar kayayyakin noma ta hanyar sarrafawa da bunkasa kasuwancin noma domin karfafa tattalin arzikin jihar.
“Ba za mu ci gaba da fitar da kayan amfanin gona ba tare da sarrafa su ba. Makoma tana cikin kara darajar kayayyaki a matakin al’umma,” ya ce.
A bangaren ilimi kuwa, gwamnan ya bayyana kokarin gwamnatin wajen rage gibin ilimi da fadada damar samun ilimi musamman a yankunan da suka fi fama da matsalar rashin ci gaba.
Ya bayyana cewa karkashin shirin Danmodi Students Care Initiative, dalibai 131 cikin 150 daga kananan hukumomin da suka fi fama da matsalar ilimi sun samu sharudan shiga manyan makarantu bayan horaswa ta musamman.
Ya ce za a tura daliban zuwa cibiyoyin koyon aikin jinya da ungozoma a jihar Jigawa, sannan bayan kammala karatunsu za su koma yankunansu domin karfafa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.
Gwamna Namadi ya kuma yi magana kan kokarin hada ilimin addini da na zamani ta hanyar shirye-shiryen horaswa ga malaman Alkur’ani.
“Kwannan nan malaman Alkur’ani 150 sun samu horo na musamman karkashin shirin da Hukumar Tsangaya ta Jihar Jigawa ke gudanarwa tare da hadin gwiwar NBAIS. Yawancinsu sun samu takardun shaidar da suka yi daidai da kammala makarantar sakandare.”
Ya ce wadannan kokari na taimakawa wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta tare da hada ilimin addini da na zamani.
A bangaren bunkasa matasa kuwa, gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na samar wa matasa hanyoyin dogaro da kai ta hanyar noma, sana’o’i da horas da su dabarun sana’a.
“Ta hanyar shirin Rice Millionaires Programme, mutane da dama yanzu suna samun kudin shiga mai dorewa daga noma kuma ba sa neman kananan ayyuka a wasu wurare,” in ji shi.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kafa cibiyoyin koyar da sana’o’i domin koyar da matasa walda, kere-kere, dinki da sauran sana’o’i.
“Wadannan shirye-shirye an tsara su ne domin bai wa matasa damar samun sana’a da rayuwa mai dorewa.”
A karshe, Gwamna Namadi ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Jigawa za ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin bunkasa ci gaban yankuna da inganta rayuwar al’umma.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version