Jihar Jigawa da IITA Sun Ƙara Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Bunƙasa Noma
Gwamnatin Jihar Jigawa na ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da Cibiyar Binciken Noma da hukumar dake kula, da sassan da suke d yanayin, Zafi ta Duniya (IITA) da ke Ibadan,
Wannan tsari na cikin ƙudurin Gwamna Malam Umar Namadi na sauya fasalin harkar noma a jihar.
An bayyana hakan ne yayin da wata babbar tawaga daga IITA, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Darakta Janar na cibiyar, Mista Abdoulaye Tahirou, wanda ya wakilci Darakta Janar, yayin da
ta kai ziyarar ban girma zuwa Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Tawagar ta nuna matuƙar godiya ga Gwamnatin Jihar Jigawa bisa kyakkyawar tarba da aka yi musu, tare da jaddada aniyarsu ta yin aiki tare domin cimma manufa guda.
Mista Tahirou ya bayyana cewa tun bayan isowarsu jihar, ta gudanar da bincike mai zurfi da jami’an gwamnatin jihar, wanda ya haifar da samar da ingantaccen shirin sauya fasalin noma
Wanda da ya dace da buƙatun Jigawa kuma mai sauƙin aiwatarwa.
Ya ce, “Mu a matsayinmu na abokan hulɗa na fasaha, mun shirya tsaf mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Mai Girma Gwamna da al’ummar Jihar Jigawa domin aiwatar da wannan shiri.”
Ya ƙara da cewa tawagar ta ƙunshi ƙwararru a fannoni daban-daban kamar haɓaka amfanin gona, abinci mai gina jiki, kimiyyar ƙasa, tsarin iri, da muhimman amfanin gona da ake nomawa a jihar.
Haka kuma, ya roƙi gwamnatin jihar da ta daidaita batun mallakar filin ƙasar da IITA ke amfani da shi a Jigawa wajen ayyukan bincike tsawon kusan shekaru 25, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar da ke tsakanin ɓangarorin biyu.
A nasa jawabin, Gwamna Malam Umar Namadi ya tarbi tawagar da hannu biyu, inda ya bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci kuma ta zo a kan lokaci, musamman bayan ziyarar da gwamnatin jihar ta kai hedikwatar IITA kwanan nan.
Gwamnan ya tuna da yadda ya yi matuƙar burgewa da kayayyakin more rayuwa da kuma ƙwarewar ma’aikatan IITA, yana mai bayyana cibiyar a matsayin wadda ke da ƙwarewar da za ta iya sauya fasalin noma ba a Jigawa kaɗai ba, har ma a faɗin Najeriya.
Ya ce, “Noma shi ne ginshiƙin tattalin arziƙinmu, kuma manomanmu ƙanana suna da matuƙar muhimmanci a gare mu. Domin ƙarfafa su yadda ya kamata, dole ne mu haɗa tsare-tsaren gwamnati da goyon bayan ƙwararru na fasaha, shi ya sa wannan haɗin gwiwa da IITA ke da matuƙar muhimmanci a gare mu.”
Gwamnan ya jaddada cewa Jihar Jigawa ta sake fasalta noma a matsayin kasuwanci, da nufin ƙara yawan amfanin gona tare da rage kuɗin samarwa, yana mai cewa shawarwari da jagorancin ƙwararru na da muhimmiyar rawa wajen cimma wannan buri.
Ya kuma tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin jihar a shirye take ta aiwatar da shirin aikin da aka amince da shi tare da ci gaba da wannan haɗin gwiwa, wanda ya bayyana a matsayin haɗin gwiwa mai amfani ga kowa, musamman manoma da kuma bunƙasa tsaron abinci.
A ƙarshe, Gwamnan ya gayyaci ƙwararrun IITA da su yi aiki tare da cibiyoyin binciken noma na jihar, yana mai cewa hakan zai ƙara zurfafa kirkire-kirkire da gina ƙwarewa a ɓangaren noma.

