Gwamnatin Tarayya ta Buɗe Rejistar Neman Guraben Karatu a Ƙasashen Waje na PTDF
Gwamnatin Tarayya ta sanar da buɗe fara rejistar neman guraben karatu a ƙasashen waje na shekarar 2026 ƙarƙashin Petroleum Technology Development Fund (PTDF), domin bai wa ɗaliban Najeriya damar karatun digiri na biyu (MSc) da digiri na uku (PhD) a Birtaniya, Jamus, Faransa da Malaysia.
Sanarwar ta fito ne ta shafin X (tsohon Twitter) na Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Sadarwa ta Zamani, Dada Olusegun, a ranar Litinin. Sanarwar ta ce an fara karɓar rejistar masu neman guraben karatun PTDF na ƙasashen waje na 2026.
A cewar bayanin da PTDF ta wallafa a shafinta na intanet, shirine na masu neman MSc da PhD a fannoni da suka shafi harkar mai da iskar gas, inda tsarin zai ɗauki nauyin kuɗin karatu, tikitin jirgi na zuwa da dawowa, masauki, alawus na rayuwa, inshorar lafiya, da kuɗin bincike (bench fees).
PTDF ta bayyana cewa shirin zai bai wa wanda suka samu guraben horo da kayan bincike na zamani a matakin duniya, tare da ƙarfafa ƙwarewar ’yan Najeriya a fannin mai da iskar gas.
Ga masu neman PhD a Birtaniya, an tanadi tsarin split-site, inda za a gudanar da bincike tsakanin College of Petroleum and Energy Studies, Kaduna (CPESK) da wasu jami’o’in haɗin gwiwa a Birtaniya, ciki har da Robert Gordon University, University of Strathclyde, da University of Portsmouth.
Hukumar ta jaddada cewa gurabe ne da ake tsananin gasa, inda za a tantance masu nema bisa kwarewar ilimi, shirin bincike, kasancewa cikin ƙungiyoyin ƙwararru, da kuma dacewar karatun da harkar mai da iskar gas.
Sharuddan MSc sun haɗa da samun akalla Second Class Lower (2.2) ko 2.1 a digiri na farko, kammala NYSC, iya amfani da kwamfuta, da samun Credit a sakamakon O’Level biyar ciki har da Turanci da Lissafi. Masu neman PhD kuma dole su gabatar da shirin bincike na shafuka biyar wanda zai fayyace manufofi, dabarun aiwatarwa, da hanyoyin tattara bayanai.
PTDF ta ƙara da cewa za a tantance NIN na duk masu ne
