Hon Aminu Sani Kumbotso Wanda ya Ke neman kujerar majalisar wakilai a inuwar jam, iyyar ADC ya bayyana cewar AL, ummar Nijeriya na bukatar sauyin rayuwa bisa la, akari da yadda jam, iyyar dake mulki a yanzu tayi watsi da wadanda suka zabe ta ta kirkiro wasu manufofi da talakawa base farin ciki dashi.
Hon Aminu Sani yace yanzu kan mage ya waye, AL, ummar Arewacin Nijeriya da Jihar kano suna neman sauyin siyasa, a saboda haka jam, iyyar ADC itace jam, iyyar AL, ummar kasa Nijeriya wadda zata share hawayen talakawan kasa.
Hon Aminu Sani Kumbotso ya Wanda aka zaba Dan majalisar Jihar kano daga yankin karamar hukumar Kumbotso ya bayyana cewar siyasa tana bukatar kaunar juna da Amana da rike Alkawari Dan kaiwa ga gaci.
Hon Aminu Sani ya bukaci magoya bayansa da su baiwa jam, iyyar ADC hadin Kai da goyan baya domin AL, ummar su samu Kayayyakin more rayuwa ta fuskar Dimukradiyya.
